Jaje: Rt. Hon. Abdullahi Ya Aika Tawagarsa Zuwa Unguwannin Da Ambaliyar Zuwa Ya Yiwa Barna (HOTUNA)

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu sannan kuma Jagaban Masarautar Kontagora, Rt. Hon. Abdullahi Idris Garba, wanda aka fi sani da suna Mai Solar, ya aika da tawagarsa da su kai ziyarar jimami ga al’ummar dake unguwanin da ambaliyar ruwa sama ya yiwa barna a gari da kuma kauyukar da suka kewaye garin Kontagora, a karamar hukumar Kontagora dake jahar Neja, Najeriya.

Hakan ya biyo bayan da dan majalisar ya yiwa wadanda ambaliyar ruwan saman ya yiwa barna jeje a shafukansa na musamman dake kafafen yanar gizo.

Mun samu labarin cewa ambaliyar ruwan saman ya janyo komasa baya sosai tare da asarar albarkacin noma, rushe-rushen gidaje da dokokiyin al’ummar wannan yankin.

Ga hotunan tawagar a kasa;

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *