Gidauniyyar Sarauniya Charity Foundation Ta Tallafawa Masu Jinya A Asibiti Da Kudade


Gidauniyyar Sarauniya Charity Foundation ta tallafawa majinyata 38 da kudade domin ragewa iyalan majinyata radaden kashe-kashen kudaden da su ke yi a lokacin da ma’aikatan suka kaiwa babban asibitin gwamnati dake garin Azare, a jahar Bauchi

Wacce ta kafa Gidauniyyar Sarauniya Charity Foundation sannan kuma Shugaban Gidauniyyar, Hajiya Rabi’atu, ta bayyana cewa yin hakan ya zo daidai da kudirorin Gidauniyyar

A yayin dake karen haske game da shirin Gidauniyyar ga manema labarai, Hajiya Rabi’atu, ta ce Gidauniyyar ta bada wannan tallafin ne domin taimakawa marasa karfi musamman talakawa wajen rage masu radaden kashe-kashen kudade da suka yi a asibiti.

Ta ce; “Sanin kowane mun samu kan mu a cikin wani irin yanayi inda mutane inda za ka wasu ma abinci ciyar da iyalansu na gagaransu balantana ma biyan kudin asibiti, hakan ya sa mu ka kawo wannan shirin domin tallafawa al’ummar tallakawa.

“Wannan shirin shine karo na farko da mu ke bada irin wannan tallafin. Saboda haka, a lokacin da mu ka zabi ziyartar wannan asibitin, mun tuntube ma’aikatar wannan asibitin wadanda sune suka taimaka mana wajen zaban wadanda suka cancani a basu wannan tallafin.”

“A karshe ina so na yi amfani da wannan dama wajen kira ga sauran Gidauniyya irin namu da su iya kokarin su wajen kawo irin wadannan tallafi ga al’umma domin taimakawa al’umma.” – Haj. Rabi’atu.

Ga hotunan a kasa;

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *