Yadda Ke Miyar Alayyahu

Yadda ake miyar alayyahu shi za mu koya a yau a darasinmu na girke-girke.

Abubuwan hadawa

 1. Alayyahu
 2. Tattasai
 3. Attarugu
 4. Albasa
 5. Tumatiri
 6. Maggi
 7. Kayan kamshi (citta da tafarnuwa)
 8. Namar rago
 9. Maggi star

Yadda ake hadawa

 1. Ki wanke albasa ki yayyanka kanana tare da tumatiri, sai ki daura mai a wuta ki zuba su a ciki.
 2. Ki yi jajjagen tarugu da tattasai da citta da tafarnuwa ki zuba, sai ki kawo naman ragonki ki zuba a ciki. Ki kawo maggi star ki zuba yadda zai ji, sai ki dan sa gishiri kadan.
 3. Sai ki sa ruwa ba mai yawa ba ki rufe shi ki barshi.
 4. Shi kuma alayyahu ki wanke tas, ki samo rariya ki zuba a ciki sai ki daura shi kan tukunyar naman ki rufe kamar za ki turara dambu har sai ya turara.
 5. Naman ki kuma ya tsotse ruwa a lokacin, sai ki kawo alayyahu ki zuba, sai ki juya, ki bari na kamar minti biyu zai dan ciro ruwa sai ki kwashe.

Aci da tuwo ko da shinkafa.

Hikima cikin wasu abubuwa

 1. Turara alayyahu na sashi yayi kore shar, sannan in kin zuba a girki baya buqatan sai ya dade.
 2. Dadewar alayyahu a kan wuta shi ke kawo wa yayi baki ba  kyau gani a ido.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *