Yadda Ake Indomie Dahuwar Gargajiya

Abubuwan hadawa

  1. Indomie
  2. Manja
  3. Tattasai
  4. Attarugu
  5. Alayyahu
  6. Daddawa.

Yadda ake hadawa

  1. Ki soya albasa da tattasai da attarugu sama-sama cikin manja.
  2. Ki kawo daddawa ki saka, sai ki kawo ruwa dai dai indomie din ki ki sa ka.
  3. In ruwan ya bararraka, sai ki sa indomie, ki sa maggin indomie sannan ki sa alayyahunki sai ki rufe ki bari har ya karasa nuna.

‘Yar uwa in ki ka gwada wannan… Habawa sai na ji daga gare ki. Na gode. Sai mun hadu a girki na gaba. Yes

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *