An Kama Matashi Na Sharara Baccinsa Bayan Ya Yiwa ‘Yar Shekaru 63 Fyade A Bisa Kan Gadon Dakinta (hoto)


‘Yan sanda a kasar Afirka ta Kudu sun cafke wani dan Shekaru 35 wanda ake zargi da Yiwa wata tsohuwa Fyade a yayin hakan Yayi bacci a bisa kan shimfidar ta har Sai da ‘Yan sandar suka zo suka kama shi.


A cewar Kakakin Yan sanda ya yankin, Kaftin Stephen Thakeng, ya ce wanda ake zargi ya Yiwa tsohuwa Yar Shekaru 62 Fyade a ranar Kirsimeti a Gidan ta dake Kutloanong, Odendaalsrus, Free State. 


“Tsohuwar ta kasance tana bacci a yayin da ya shigo ma ta gida ya ma ta fyade. Shi wanda ake zargi a cafke shi ne a yayin da yake bacci a dakin,” in ji Thakeng a wani sanarwa da ta hukumar Yan sanda suka fitar a ranar 26 ga Watan Disamba 2021z

“A ranar 25 ga watan Disamba 2021 da misalin karfe 10:15 ita wacce aka ci zarafin ta Tana bacci ta tashi Bayan ta ji an kwankwasa ma ta a kofarta

“Daga nan kawai ta ji muryar namiji ya umurce ta da ta tube kayanta, a nan ne ya shake ta sannan ya ma ta Fyade.

“Bayan ya ma ta fyade kawai Sai bacci ya dauke shi. a nan ne ita kuma wacce aka yiwa fyaden ta samu samar tserewa domin ta samu agaji daga wurin makwabtan ta.

An sanar da mambobin Odendaalsrus SAPS da faruwar lamarin inda a nan take suka kai dauki tare da ganin wanda ake zargi kwance yana sharara baccinsa a bisa kan gadon tsohuwar da ya Yiwa Fyade.


”’Yan sanda suka tashe dan Shekaru 25 din tare da kama shi da laifin shiga Gidan mutane ba tare da ba shi umurni ba sannan kuma da laifin aikata Fyade.

Za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban Kotun Majistare Na Odendaalsrus a ranar 28 2021

Sanarwan Da Yan Sanda Suka Fitar Game Da Lamarin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *