Hotunan Gabanin Nadin Sarautar Rt. Hon. Abdullahi Idris Garba A Matsayin JAGABAN KONTAGORA

Wannan sarautar JAGABAN KONTAGORA shine karo na farko da masarautar ke nadawa wani sarautar.

Rt. Hon. Abdullahi Idris Garba (Mai Solar) ya kasance gwarzo a cikin jaruman matasa dake karkashin masarautar a bisa irin rawar da yake takawa wajen ganin samarwa al’ummar masarautar ci gaba ta hanyoyin daban daban.

Hakan ya sa ake gayyatar al’umma zuwa taron nadin sarautar Mai Martaba Sarkin Sudan Alh. Saidu Namaska zai nadawa, Rt. Hon. Abdullahi Idris Garba, sarauta a ranar 15 ga watan Junairu, 2021 a fadarsa dake garin Kontagora a jahar Neja da misalin karfe 10:00 na safiyar.

Ga sabbin hotunan a kasa;

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *