Sabon Harin ‘Yan Bindiga Ya Hallaka Mutane Da Dama A Katsina

Da yammacin jiya Talata wasu ‘yan bindiga suka kai hari hari a wani kauye, wanda ake kira Shuwaki da ke da nisan kilomita sha biyar daga karamar hukumar Faskari, a cikin jihar Katsina, inda suka hallaka mutum hudu har lahira, suka jikkata mutum hudu wanda yanzu haka suna asibitin garin Faskari, domin amsar magani.

Wani mazaunin garin ya shaidawa RARIYA ta waya, inda yan bindiga sun zo ne da marecen nan ido-na-ganin-ido, bisa mashina dauke da bindigogi, suka fara harbe-harbe har suka kashe mana mutum hudu da raunata hudu, wadanda a halin yanzu mun kai su asibitin garin Faskari, sun kuma kwashe mana dabbobi,da a halin yanzu ba za mu iya tantance adadin su ba.

Idan dai za’a iya tunawa karamar hukumar Faskari, nan ne ke da wata runduna ta musamman ta sajoji, wadda ake kira (Sahel Sanity) wanda sansani ne na yaki da barayin shanu da satar mutane na arewa maso yamma.

RARIYA ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya ce zai bincika, har zuwa aiko da wannan rohoto bai tabbatar da wannnan ba ko akasin hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *