Kotu Ta Yi Fatali Da Buƙatar Maina

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da bukatar da Abdulrasheed Maina ya gabatar na neman a sake dage shari’arsa domin kara shiri don kare kansa.

A zaman kotun na ranar Talatar nan, Alkali Okon Abang ya ce matakin da kotun ta dauka na dage shari’ar tun da farko na daga cikin sassaucinta ne amma Mainan yana kokarin yin wasa da hankalin kotu.

Tun da farko lauyan hukumar EFCC Farouk Abdullah ya shaida wa kotun cewa an shirya za a ci gaba da shari’ar ne yayinda sabon lauyan Maina ya yi gardamar cewa suna bukatar lokaci domin ba su dade da amsar shari’ar ba.

Saidai kuma Alkali Abang ya yi bayanin cewa tun lokacin da aka ci gaba da shari’ar a ranar 29 ga watan Satumba, Maina bai bayyana a zaman kotun ba har saida aka bada umarnin kamo shi

Ya ce idan har sabon lauyan na Maina na bukatar bayanan shari’ar, to tsohon lauyansa ya kamata ya ba shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *