Hon. Abdullahi Ya Baiwa Kowane Matashi N500,000 Daga Cikinsu 245 Don Dogaro Da Kai

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu, Hon. Abdullahi Idris Garba (wanda aka fi sani da suna Mai Solar) a majalisar wakilai ta kasa ya Tallafawa matasa maza da mata da kudaden fara sana’ar yin garin wake a mazabarsa. Shirin wanda dan majalisar ya dauki nauyi ya samu hadin gwiwar Nigeria Stored Products Research Institute a bangaren horas da matasan.

An samu labarin hakan ne daga bakin Dan Majalisar a shafinsa na yanar gizo ta Facebook.

Wannan shine bikin yaye matasan da aka horas tare da bada tallafin kudade ga matasan domin fara nasu Kasuwancin don dogaro da kai

Akalla matasa 245 suka ci moriyar wannan shirin sannan kuma bayan sun kammala dan majalisar ya basu kudade fara sana’ar yin garin wake inda dan majalisar ya baiwa matasa 31 naira N500,000, ya baiwa wasu 2 Naira N300,000, ya baiwa wasu daga cikin su naira N200,000 a yayin da ya baiwa sama da 174 Naira N100,000 ga kowannensu; idan aka Hada sun kama mutane 245 kenan wadanda kowane daga cikinsu sun kasance daga wurare daban daban dake ke fadin mazabar dan majalisan.

A yayin da Dan Majalisa Abdullahi Idris Garba ke magana da Yan jarida ya bayyana cewa an gudanar da Shirin ne domin a shigar da matasa maza da mata ga harkar Kasuwancin garin wanke wanda kasuwancinsa ke dada bunkasa a fadin kasar da ma a kasashen wajen sannan kuma hakan zai taimakawa tattalin arzikin tare da samarwa matasa aikin yin.

A karshe dan majalisan Yayi kira ga matasan da suka ci moriyar wannan shiri da su yi amfani da damar da suka samu wajen yin amfani da ilimin da aka horas da su a harkar sana’ar da aka horas da su tare da amfani da kudaden da aka basu wajen yin wannan sana’ar

Ku kalli Hotunan A kasa;

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *