Hon. Abdullahi Idris Garba Ya Yi Allah Wadai Da Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai A Wushishi

Hon. Abdullahi Idris Garba da harin da wasu ‘yan bindiga suka kaiwa ‘yan kasuwa dake Sabon Gari ward, Tashar Mota wanda sanadiyyar hakan ya sa suka kashe wasu yara mata 2 tare da yin awon gaba da wani yaron shago daya.

Dan Majalisa Abdullahi ya nuna damuwarsa musamman ga irin yadda ‘yan bindiga suka soma addaban wasu wurare dake karkashin mazabarsa dama jahar ga baki daya.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a yayin da yayi hira da daya daga cikin wakilan mujallar yanar gizon Gulmawuya inda ya bayyana cewa gwamnatin kasa dake karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari tare da Gwamnatin jahar Neja karkashin jagorancin Alh. Dr. Abubakar Sani Bello (Abulolo) suna nan suna iya kokarinta wajen ganin Kawo karshen ta’addanci da fadin jahar dama kasa ga baki daya.

JaDan majalisar ya ce yana iya iyayen yaran da suka rayukansu ta’azziyya inda yayi addu’ar Allah ya rahamshe su.

A karshe kuma “ ina mai kira alummar mazabarta da ma kasa ga baki daya su taimakawa gwamnatin wajen yin addu’a kawo Karshen wannan yanayi da mu ka tsinci kan mu a ciki tare da baiwa hukumomin Tsaro hadin kai” – Inji dan majalisar Hon. Abdullahi Idris Garba (Mai Solar)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *