Hon. Abdullahi Idris Garba Ya Kaddamar Da Shirin Horas Da Matasa 245 A Kan Sarrafa Garin Wake Don Dogaro Da Kai

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu a majalisar wakilan tarayya, Hon. Abdullahi Idris Garba (wanda aka fi sani da suna Mai Solar) tare da hadin gwiwar Nigeria Stored Product Research Institute sun horas da mata da matasa 245 a kan sana’ar sarrafa garin wake ja da fari domin dogaro da kai.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a shafinsa dake yanar gizo

A yayin da wakilin mujallar yanar gizon Gulmawuya ya tattauna da Shugaban kula da harkokin da suka shafi wannan Shirin, Alhaji Musa Dabai, yayi karin haske game da Shirin.

Alhaji Dabai ya kara da cewa bayan an gama horas da matasan game da sana’ar dan majalisar zai baiwa kowanne daga cikinsu ba kudi domin su fara sana’ar da kansu.

A wannan shekarar kawai dan majalisan ya horas da matasa sama 1,000 sana’o’i daban daban tare da basu tallafin kudade domin dogaro da kai. Hakan na Cikin kudirorin fan majalisan a bangaren rage radadin tallauci tare da sama war matasa aikin yi.

Ga Hotunan a kasa;

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *