FCE Kontagora Ta Karrama Hon. Abdullahi Idris Garba Da Lambar Yabo

Kwalajin Ilimi na Gwamnatin Tarayya dake Kontagora (FCE Kontagora) ta karrama dan majalisa mai wakiltar mazabar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu a majalisar wakilai na kasar Najeriya, Hon. Abdullahi Idris Garba (wanda aka fi sani da suna Mai Solar) da lambar yabo a bisa kokarin da yake yankunan mazabarsa.

An samu wannan labarin ne a yayin da dan majalisar ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya yiwa hukumar kwalejin godiya ta musamman.

An baiwa lambar yabon ne a ranar da kwalejin ta buga tare da sako littafin makarantar.

Lambar yabon ya fito daga kungiyar lakcarorin kwalejin inda Kungiyar ta jaddada shaidar kokarin da dan majalisa Abdullahi Idris Garba (Mai Solar) ya kai wajen samar da ci gaba a duk fadin mazabarsa.

Dan majalisar ya nuna farin cikinsa a bisa irin karrama shi da aka yi sannan ya kuma lashi takobin kara hazaka.

Dan majalisar ya samu wakiltar Barista Lawal Yusuf a ranar taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *