ZAƁEN 2023: Na Amsa Kiranku, A Shirye Nake In Tsaya takara – Okorocha

Sanatan da ke wakiltar gundumar sanatocin Imo ta Yamma kuma tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, a jiya, ya ce lokaci ya yi da ya kamata shugabancin Najeriya ya fito Daga ƙabilar Ibo.

Okorocha ya ce, “Na karanta saƙon Da Wasu Masoya na suka aike min da shi Cewa kuna son in fito takarar shugabancin Najeriya Daga Ƙabilar Ibo. Kuma kun ga na cancanci wannan matsayin. Ina jin girmamawa kuma ina farin ciki.”

“Bari na gaishe ku ta yadda kuka tafiyar da kanku cikin kwanciyar hankali kuma wannan abin a yaba ne.

“A wurina, na yi takarar wannan ofishi na shugaban kasa ta hanyar amfani da jam’iyyun siyasa daban-daban kuma har sau uku a da na Tsaya takarar ofishin shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ANPP, kuma karo na biyu a karkashin PDP, na uku a APC, kuma yanzu Idan har ya zama dole in sake tsayawa to zan Ɗan natsa kafin in ambaci jam’iyyar Da zan Fito a cikin ta Saboda hadin kan ‘yan Najeriya.

Idan har zan tsaya takara, to zai zama ne domin karfafa matasa a Najeriya, idan kuma ya zama dole na tsaya takarar shugaban kasa, hakan zai sa wannan al’ummar ta yi gogayya da sauran manyan kasashen duniya ta fuskar tattalin arziki”, Inji shi.

Ya kuke kallon wannan Ƙudiri Na shi?

Dimokuraɗiyya Adon Ƙasa!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *