Babu Gaskiya A Labarin Harbo Jirgi A Borno – Rundunar Soji

Rundunar sojojin saman Najeriya, NAF, ta ƙaryata rahoton da kafafen watsa labarai suka wallafa na cewa Boko Haram to harbo jirgi mai saukan ungulu a Borno ta kashe mutum biyar.

Rahoton ya bazu sosai a shafukan intanet a yammacin jiya cewa ƴan ta’adda sun harbo jirgi mai saukan ungulu a Banki, wani gari da ke Borno wadda ya yi sanadin rasuwar mutum biyar.

A martanin da ya yi ta shafin Twitter, Shugaban sashin watsa labarai da hulda da jama’a na rundunar Air Commodore Ibikunle Daramola ya ce rahoton ba gaskiya bane.

“Babu wani jirgi mai saukan ungulu a jihar Borno da aka harbo a yau. Wani jirgi mai saukar na majalisar dinkin duniya ya tafi Banki kuma tuni ya dawo Maiduguri.”

Kazalika, hadimin Shugaba Muhammadu Buhari a fanin sabuwar kafar watsa labarai, Bashir Ahmad shima ya yi tsokaci kan labarin. Ya bayyana cewa labarin ba gaskiya bane kana ya shawarci kafafen watsa labarai su rika tantance labari kafin su wallafa.

Ya ƙara da cewa idan kuma sunyi kuskure kamata ya yi su wallafa wani labarin su gyara kuskuren don al’umma su san gaskiyar lamarin ba suyi shiru su cire labarin ba daga shafinsu kawai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *