Korona: Mutane 152 Sun Sake Harbuwa – NCDC

Sabbin alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa NCDC na ranar Lahadi sun bayyana cewa sabbin mutum 152 sun sake harbuwa a Najeriya.

Kamar yadda alkalumman suka bayyana, an samu mutane…

136 a jihar Legas

4 a jihar Kano

3 a jihar Neja

Sai 2 a jihar Ekiti

Jimillar mutanen da suka taba kamuwa da muguwar cutar a Najeriya sun kai mutum 65148 a fadin kasar nan Kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta bayyana na ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamban 2020.

Wadanda aka sallama daga asibiti bayan warkewarsu sun kai 61073, yayin da mutum 1163 suka riga mu gidan gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *