Katsina: Masari Zai Ciwo Bashin Naira Biliyan N50

Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta fara wani shiri na karɓo bashin Naira biliyan 50 domin yin wasu ayyuka a cikin shekarar 2021.

Kwamishinan kasafin kuɗi da tsare tsaren tattalin arziki na Jihar Hon. Faruk Lawal Joɓe ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswar jihar a ranar Laraba.

Kamar yadda ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen kammala wasu ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ta fara.

Haka kuma, kwamishinan ya ce a zaman majalisar zartaswar an amince da Naira biliyan 283 a matsayin ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2021.

Kuna ganin Ciwo bashin makudan kudade ya dace a halin yanzu ga jihar katsina? Muna sauraran ra’ayoyin ku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *