An Ceto Wasu Daga Cikin Mutanen Da Aka Sace A Hanyar Abuja

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar kaduna Samuel Aruwan ya fitar da sanarwar cewa jami’an tsaro sun ceto mutane 9 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna zuwa Abuja da rana tsaka a Lahadin da ta gabata.

Jami’in na gwamnatin Kaduna wace ta sanya hotan mutanen da aka ceto a Facebook ya ce abin takaici mutum biyu sun rasa rayukansu, bayan da barayin suka fara tare mota kirar Bus mai fasinja 18. A cikinsu ne kuma direba da na kusa da shi suka rasu, yayinda jami’an tsaro suka bi barayin cikin daji wurin karfe 4 na yamma inda kuma suka yi nasarar ceto mutane 9 da ‘yan bindigar suka sace.

A yammacin jiya Lahadi ne wannan lamarin ya faru a daidai hanyar abuja zuwa kaduna a wani gari mai suna katari inda hakan ya sanya daruruwan motoci yin cirko cirko bayan da barayin suka sanya shinge da rana tsaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *