Ƙetare: Trump Ya Amince Da Shan Kaye A Hannun Biden

A karshe, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya amince cewa ya sha kaye a hannun abokin hamayyarsa, Sanata Joe Biden, a wani yanayi na bazata.

A wani sako da ya wallafa ranar Lahadi, Trump ya yarda Biden ya samu nasara amma ta hanyar tafka magudin zabe.
“Ya samu nasara ne saboda an tafka magudi a zaben. Babu masu sa-ido, babu masu lura da zabe. An yi amfani da wani kamfani da sunansa ya gurbata wajen tattara sakamakon zabe.

Kafafen yada labarai da ke yada labaran bogi, da wadanda suka yi shiru, suka ki yin magana, duk sun taimaka wajen danne nasarar da na samu a Texas,” kamar yadda Trump ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Trump ya yi ikirarin samun nasara a daren da aka kammala zaben shugaban kasar Amurka.

A cikin makon da ya gabata ne muka ruwaito muku cewa sakataren gwamnatin ƙasar Amurka, Mike Pompeo ya ce ƙasar Amurka zata yi amfani da dukkan makaman da take dasu don yaƙar ta’addanci a Najeriya da yammacin Afirika.

Ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da haɗakar kasashen duniya (GCD) don cin galabar ƙungiyar ISIS wanda ƙasar Najeriya ta kasance mai masaukin baƙi.

A cewarsa, an samu gagarumar nasara a tattaunawar ganawa da gwamnatin Najeriya. “An samu gagarumar matsaya da nasara a tattaunawa da gwamnatin Najeriya a taron haɗakar ƙasashen duniya don cin galabar ISIS da makamantan ƙungiyoyi irinta a ko ina a faɗin duniya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *