Sarki Bamalli Zai Sauya Fasalin Masarautar Zazzau

Majalisar masarautar Zazzau karkashin jagorancin Sabon Sarkin Zazzau Anbasada Ahmed Nuhu Bamalli ta ce nan ba da dadewa ba zata aikewa gwamnatin jihar Kaduna bukatar ta na sake fasalta masarautar zazzau don inganta ayyukanta.

Mai martaba sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu-Bamalli ne ya bayyana hakan ne yayin da mataimakiyar gwamnan jihar Dr Hadiza Balarabe ta jagoranci tawagar jami’an gwamnatin jihar don kai ziyarar girmamawa a fadar ta Zazzau.

Mai martaba sarkin ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta sake yin nazarin ayyukan masarautun da ke fadin jihar ta yadda za ta kara inganta su.

A karshen makon da ta gabata ne dai aka mika ragamar mulkin masarautar Zazzau ga Sabon Sarkin Zazzau Anbasada Ahmed Nuhu Bamalli bayan rasuwar marigayi mai martaba Shehu idris a ranar 20 ga watan Octobar wannan shekara da muke ciki.

Hausawa na cewa sarki goma zamani goma. Kuna ganin sauya fasalin masarautar shine abinda ya dace da sabon Sarkin ko kuwa akwai abinda yafi hakan muhimmanci a gareshi?

Za muso jin ra’ayoyin ku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *