Gombe: Gwamnati Ta Ɗauki Nauyin Aikin Wanda Ya Yi Tattaki Zuwa Abuja

Biyo bayan wassu rahotannin kafafen watsa labarai game da Ɗahiru Buba ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Dukku a Jihar Gombe wadda ke fama da ciwon ƙafa bayan tattakin da yayi daga Gombe zuwa Abuja don taya shugaba Buhari murnar sake lashe zaben 2019, Gwamnatin Jihar Gombe ta ɗauki nauyin duba lafiyar mutunin a wani asibiti tare da yi masa jinya.

Idan za a iya tunawa dai kafafen watsa labarai sunyi ta yayata kiraye-ƙirayen da Ɗahiru Buban yayi tayi ga jama’a da masu hanu da shuni kan su taimaka masa bisa fama da ciwon gwiwa da yake yi, biyo bayan tattakin murna da nuna goyon baya da yayi don taya shugaba buhari murnar sake lashe zaɓe karo na biyu.

Bisa umarnin da mai girma Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayar, an ɗauki Ɗahiru Buba zuwa asibitin gidan gwamnati, inda daga bisani aka maida shi wani asibitin ƙashi inda aka ƙalailaice ciwon nasa aka kuma ɗora shi kan magani.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zagayen farko na jinyar da ake masa, Ɗahiru Buba ya godewa Gwamna Inuwa Yahaya bisa kai masa ɗauki cikin gaggawa.

Yace ya fara jin ba daidai ba ne bayan dawowarsa gida daga tattakin na kwanaki 15 da yayi zuwa Abuja.

Alhaji Ahmad Yahaya da Isa Faruk waɗanda suka taimaka wajen ɗauko majinyacin daga Dukku zuwa Gombe, suka ce Ɗahiru yayi fama da matsanancin ciwon ƙafa bayan dawowarsa daga tattakin taya murnar.

Sai suka bayyana farin ciki da kyakkyawan fata cewa “Ganin yadda Gwamnatin Jihar Gombe ta kawo wa ɗan talikin ɗauki, suna sa ran Ɗahiru Buba zai samu kyakkyawar kulawar jinya yadda ya kamata”.

Sai suka bayyana karamcin na Gwamna Inuwa da cewa wani abun farin ciki ne da ya zo musu da ba zata, suna masu addu’ar Allah ya biya shi da mafificin alkhari.

Sun kuma yaba da irin tallafin da kwamishinan kuɗi na jihar Muhammad Gambo Magaji ya yiwa iyalan majinyacin, wadda suka ce ya nuna damuwa da kulawa sosai tun daga lokacin da ya fahimci halin da Ɗahiru Buban ke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *