Babban Kuskure Ne Afuwar Da Gwamnati Ke Yi Wa ‘Yan Boko Haram – Majalisa

Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da cewar ta yi koyi da takwararta Haɗaɗɗiyar daular Larabawa, UAE, wajen zaƙulo masu ɗaukar nauyin Boko Haram a Najeriya don ɗaukar matakin ladabtarwa da gaggawa.

Sanatocin sun kuma yi kira ga rundunar sojin Najeriya da ta tayi watsi da bawa tubabbun ƴan Boko Haram kariya waɗanda suke da hannu dumu dumu wajen kisan kiyashi da lalata dukiyar al-umma,inda suka ce tsarin kwata kwata ba dai-dai bane.

Da yake magana da ƴan jaridu jim kaɗan bayan ganawar sirri da shugaban rundunar Soji, Janaral Yusuf Buratai akan shawarwarin kasafin kuɗin tsaro na shekarar 2021,shugaban kwamitin Sanatoci akan rundunar Soji, Sanata Ali Ndume, ya ce ƙasar haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi aiki mai kyau, abin koyi.

A farkon makon nan ne kasar Daular Larabawan ta ɗaure waɗanda ake zargi da ɗaukar nauyin Boko Haram, inda yace ana jan ciki wajen yankewa masu irin wannan laifi hukunci a Najeriya.

Ya ƙara da cewa ba tubabbun ƴan Boko Haram kariya na iya kawo naƙasu a yaƙin da ake da ta’addanci.

“Muna yabawa gwamnatin haɗaɗɗiyar Daular Larabawa kuma har yanzu muna roƙon gwamnatin mu kan ta zaƙulo masu ɗaukar nauyin ƙungiyar a fili ko a ɓoye don gurfanar da su gaban kuliya cikin hanzari.
“Ba mu yarda da ba tubabbun ƴan Boko Haram kariya ba, Matsayar ɓangaren zartarwa daban, bazai yiwu ku rinƙa shagwaɓa tubabbun ƴan Boko Haram ba da jindaɗi, su kuma wanda ayyukansu ta shafa ku barsu a sansanin ƴan gudun hijira, hakan ba adalci bane.

“Har yanzu Muna kira ga gwamnatin Najeriya da ta zaƙulo masu hannu a ɗaukar nauyin Boko Haram a zahirance ko a baɗini don yin misali akansu don ya zama izina ga masu aikata ta’addanci.

“Ban yarda da gwamnatin Najeriya ba akan sauyawa tubabbun ƴan ƙungiyar suna da kuma yafe musu laifukansu, saboda basu cancanci hakan ba. “Ba zai yiwu ba ace kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi, su ne da laifi kuma sune da jindaɗi, inda su kuma waɗanda abin ya shafa ko oho.

Na yarda cewa dani da sauran ƴan Najeriya masu yawa matsayar mu ɗaya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *