Shugaban Hukumar Zaɓe Ya Ajiye Muƙami

Shugaban Hukumar zaɓe mai zaman kanta Farfesa Mahmoud Yakubu ya sauka daga kujerarsa a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) bayan karewar wa’adin shugabancin shi.

Ya mika ragamar shugabanci ga kwamishinan zabe na kasa, Air Vice Marshal Muazu Ahmed mai ritaya, a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, kamar yadda dokar Hukumar ta tanada.

Hakan ya gudana ne a wajen wani taro da aka gudanar a hedkwatar hukumar zaben da ke Abuja, babbar birnin tarayyar kasar, kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter.

Ahmed zai yi aiki a matsayin Shugaban rikon kwarya har zuwa lokacin da Majalisar dattawa za ta tabbatar da sake nada Farfesa Yakubu a matsayin shugaban INEC.

A baya mun kawo muku cewa Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu zai mika ragamar ma’aikatar ga wani baturen zabe da zai yi rikon kwarya, har sai majalisar tarayya ta tabbatar da kara nadinsa a matsayin shugaban INEC din ko kuma akasin hakan.

Bayan shugaba Muhammadu Buhari ya kara zabar Yakubu, ya mika sunansa ga majalisar tarayya don tabbatar dashi, dama wa’adin mulkinsa na farko zai kare ne a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *