Najeriya Na Buƙatar Addu’a – Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, ta bukaci a sanya kasar Najeriya a addu’a, ta la’akari da yadda abubuwa masu sanya damuwa da takaici ke ƙara dumfaro ƙasar.

Aisha Buhari ta yi wannan kiran ne a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani na Instagram a ranar Labara 11 ga watan Nuwamban 2020.

Uwargida Aisha ta ƙara da cewar yadda abubuwa suke faruwa a ƙasar ya zama dole jama’a su koma ga Allah tare dagewa wajen gudanar da addu’o’i domin samun mafita.

“Allah ya isar mana kuma shine mafi alkhairin jagora. Shine mai bada kariya da kuma taimako.”

A wani labari na daban, shugaba Muhammadu Buhari ya ce matsawar yana kan mulki, ‘yan Najeriya ba za su yi kukan rashin abinci ba.

Domin za a cigaba da noma don samar da abinda kowa zai kai bakin salatinsa. Shugaban kasar, ya fadi hakan a wani taro wanda NALDA ta shirya a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamba.

An shirya sabon tsarin don taimakon matasa a kan harkar noma. Shugaba Buhari ya ce zai yi iyakar kokarinsa wurin ganin ya bunkasa tattalin arzikin kasa wurin sayar da kayan gona ga kasashen ketare.

Shugaba Buhari ya ce yana so a dawo da noma a duk gonaki da aka dena noma acikinsu don bai wa matasa maza da mata damar yin noma.

A cewarsa, mulkinsa zai tabbatar an samu habaka a harkar noma, kuma hakan zai bayar da damar samun wadataccen abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *