Har Abada Najeriya Ba Za Ta Manta Balarabe Musa Ba – Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fitar sanarwar ta’aziyya ga al’ummar Najeriya da jihar Kaduna kan rasuwar tsohon gwamnan wanda ya bayyana a matsayin muryar masu rauni….

Shugaban ƙasa ya bayyana cewar har abada Najeriya ba za ta manta irin gudunmawar da Balarabe Musa ya bayar ba wajen haɓakar siyasa da inganta rayuwar jama’a musamman masu ƙaramin karfi.

Yayin da yake addu’ar neman masa gafarar Allah, Shugaba Buhari ya ce marigayin ya yi wani gagarumin tasiri a dimokraɗiyyar ƙasar kuma ya taka gagarumar rawa wajen tabbatar da kyakkyawan shugabanci da ci gaban al’umma da ƴan kasar za su riƙa tuna shi tare da gode masa a ko da yaushe.

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-rufai ya ce za a tuna Balarabe Musa a matsayin ɗan siyasa mai son ci gaban al’umma wanda kuma ya faɗaɗa hanyoyin samun damarmaki ga talakawa.

Balarabe Musa wanda shi ne gwamnan farar hula na farko a tsohuwar jihar ta Kaduna – ya rasu ne a ranar Laraba bayan ya yi fama da jinya.

Ya zama gwamna ne 1979 a ƙarƙashin jam’iyyar PRP, ko da yake an tsige shi a 1981 kafin ya kammala wa’adinsa.

Marigayin na cikin manyan ‘yan siyasar Najeriya da suka taka rawa wajen tabbatar da mulkin dimokuradiyya.

Balarabe Musa ya shafe rayuwarsa a jam’iyyar adawa inda ya ci gaba da taka rawa a harkokin siyasa da bayyana ra’ayoyinsa kan yadda ake tafiyar da Najeriya.

Marigayin na cikin manyan ‘yan siyasar Najeriya masu ra’ayin sauyi da suka taka rawa wajen tabbatar da mulkin dimokraɗiyya ta hanyar nuna rashin amincewa ta zahiri da mulkin soja.

An haife shi ne a watan Agustan shekarar 1936 a garin Kaya dake yankin ƙaramar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna, ya yi karatu a cibiyar nazarin harkokin mulki da gudanarwa da ke Zaria da kuma wasu makarantu da ke birnin London.

An zaɓe shi gwamnan jihar ta Kaduna ne a 1979 a ƙarƙashin jam’iyyar PRP, mai rajin ceto talaka daga mulkin danniya. Ko da yake an tsige shi a 1981 kafin ya kammala wa’adinsa.

Amma duk da haka ya ci gaba da taka rawa a harkokin siyasa da bayyana ra’ayoyinsa kan yadda ake tafiyar da Najeriya inda har ya jagoranci wata tafiya ta ƙalubalantar gwamnatin soji ta Marigayi Janar Sani Abacha da zummar ganin an mayar da kasar kan tafarkin dimokuraɗiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *