Boko Haram: Wankin Hula Ya Kaimu Dare – Gwamna Bala

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya nuna takaicinsa a kan yadda yakar Boko Haram yake daukar lokaci mai tsawo, abubuwa suna tafiyar Kura a koda yaushe.

Gwamnan jihar Bauchin ya bayyana hakan ne yayin da kwamitin ‘yan majalisar wakilai a kan sojoji suka kai masa ziyara a gidan gwamnati a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, ya ce wannan babban abin kunya ne a ce har yanzu ba a kawo karshensu ba.

“Ku taimaka, ku samar mana da kwanciyar hankali. Idan ba a kawo karshen wannan al’amarin ba, zai zama abin kunya. An dade ana yin abu daya.”

Sannan ya yi tsokaci a kan tsanantuwar ‘yan ta’adda da masu satar shanu wanda ya janyo sojoji suna ayyukan ‘yan sanda, inda ya bayyana hakan a matsayin abin kunya.

“Sojoji kullum bukatar makamai da kayan aiki suke yi, sun gaji, saboda ba za ka hada yawansu da na ‘yan Najeriya ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *