Boko Haram: Mun Kashe Biliyan Biyu Da Rabi Wajen Addu’o’i – Dasuƙi

Jami’in binciken hukumar hana almundahana da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Adariko Micheal, a ranar Laraba ya bayyana abinda aka yi da kudin makaman da ake zargin Dasuki da karkatarwa.

Micheal ya ce an kashe naira 2.2 billion kan addu’ar kashe karshen Boko Haram a Nijeriya da Sauidyya, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Jami’in ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a matsayin shaida a kotu a shari’ar Sambo Dasuki, tsohon mai baiwa kasa shawara lokacin gwamnatin Jonathan wanda ake zargi da wawushe kudin makamai dala bilyan biyu.

Sambo Dasuƙi dai shine mai bada shawara akan harkokin tsaro zamanin mulkin tsohon Shugaban ƙasa Jonathan, kuma ya lashe tsawon shekaru yana garkame a gidan yari a mulkin Shugaban ƙasa Buhari, kafin sakin da aka yi mishi daga baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *