2023: Mace Ya Kamata Ta Shugabanci Najeriya – Amina Mohammed

Mataimakiyar babban sakataren majalisar dinkin duniya, Hajiya Amina Mohammed, ta bayyana cewar Mace ya kamata ta shugabancin Najeriya a shekarar 2023, saboda haka ta bukaci Mata da su dage wajen ganin sun karbi mulki daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Amina Mohammed, wacce ta jagoranci wata tawagar manyan jami’an majalisar dinkin duniya a ziyarar da suka kawo Najeriya, ta bayyana hakan ne yayinda take jawabi a wani shirin gidan talbijin a Abuja.

A ranar Litinin ne manyan jami’an majalisar dinkin duniya suka gana da Shugaban kasar a fadar Shugaban ƙasa Aso Villa a Abuja kan dabarun farfadowa bayan koma bayan da annobar COVID-19 ta haddasa.

Da take magana a ranar Talata, Amina Mohammed ta ce ya zama dole dukkanin ‘yan Najeriya su hada kai don sake gina kasar, ba tare da la’akari da banbancin kabila ko siyasa ba, ko kuma addini ba.

“Akwai bukatar mu gane abunda yake ba daidai ba, mu yi aiki don ganin mun cimma nasara sannan mu san cewa za mu iya hakan ne a tare, kowannenmu na da hakki,” in ji ta.

Ta kara da cewa akwai bukatar mutunta kowane yanki na kasar nan “dukkaninmu muna da gudunmawar da za mu bayar.”

Mataimakiyar Sakataren majalisar dinkin duniyar ta bayyana cewa Najeriya na iya samar da irin shugabanci da Afrika ke so ta hanyar aiki wajen cimma tsare-tsaren ci gaba mai dorewa na UN17 a 2030.

Da aka tambayeta ko za ta so mace ta gaji Buhari a matsayin Shugaban Najeriya, babbar jigon ta Majalisar Duniya ta ce: “Wannan shine burina kuma ina ganin mace za ta iya.

A koda yaushe mutum ya jajirce wajen neman wannan takara kuma kada ya gaza wajen gwada sa’arsa. “Saboda haka, mata su tashi tsaye. Sune ke da kaso 50 na kuri’u sannan idan har za su iya nuna bajinta kamar namiji, mazan za su mara wa mata baya, toh mai zai hana?.

Babu wani dalili da zai hana mace iya jagorantar Najeriya.” Tsohuwar ministar muhallin ta Najeriya ta kara da cewa: “imma mace ko namiji abunda muke bukata shine dan Najeriya, mutum da ke kallon kasar nan a yadda take cikin hadin kai da karfinta da kuma tattauna hanyar kai ta ga mataki na gaba.

“Sai mun motsa daga magana da baki kawai zuwa aiwatarwa a aikace a dukkan kananan hukumomi 774, jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja. Wannan shine aikin da ake da bukatar yi kuma za a iya yi a karkashin shugabancin mace.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *