Kuɗin Fansa Muka Biya: Ba Gwamnatin Zamfara Ta Ceton ‘Ya’yanmu Ba – Iyayen Yara

Al’ummar Dan-Aji da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, inda ‘yan bindiga suka sace wasu ‘yan mata 26, dun karyata ikirarin da gwamnatin jihar Zamfara ta yi, na cewa ba a biya kudin fansa kafin sako ‘yan matan ba.

Wasu majiyoyi sun shaidawa Daily Trust a ranar Litinin cewa, sai ranar 6 ga watan Nuwamba aka sako ‘yan matan, bayan an sace su, a ranar 13 ga watan Oktoba a garin na Dan-Aji, wanda ke kan iyaka da jihar Zamfara.

A karshen mako ne dai, wakilan gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Alhaji Abubakar Dauran, suka mika ‘yan matan 26 ga gwamna Aminu Bello Masari na Katsina.

A daren ranar Litinin ne, mai taimakawa gwamnan kan yada labarai da wayar da kan jama’a, Zailani Bappa, ya shaida wa Daily Trust cewa an ceto ‘yan matan ne ta hanyar sulhu da ‘yan bindigar.

Saidai kuma Dagacin kauyen na Dan-Aji Alhaji Lawal Dogara ya shaida wa ‘yan jarida a Katsina cewa sai da suka biya Naira miliyan shida da dubu dari shida sannan aka saki ‘yan matan.

Ya ce shugabannin kauyen guda biyu, Alhaji Abdulkarim Dan Aji da Liman Babangida Dan-Aji, sai da suka yi tafiyar kwana uku cikin daji a kafa, sannan suka kai wa ‘yan bindigar kudin a cikin daji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *