Hon. Abdullahi Ya Kaddamar Da Shirin Gina Asibiti A Tashar Jirgi Dake Karamar Hukumar Wushishi

HON ABDULLAHI IDRIS GARBA (MAI SOLAR). Dan Majalisa mai wakiltar Hukumomin Kontagora, Mariga, Mashegu da Wushishi a majalisar tarayya dake Abuja.

Abisa kokarinsa na samarwa mutanen yankin sa waje na bangaren Lafiya, Ya Kaddamar da gina Asibiti a Tashar Jirgi (Wushishi Local government)

Mal. Shehu Ciroma da Sauran Committee members na Mai solar ne suka bayyana a Tashar jirgi Wushishi tare da Manyan Mutani na Yankin, wanda ya hada da Mai unguwa “Malan Muhammad Lawal”, Sarkin Noma, Former da dai sauran su.

Mai Unguwan Tsahar Jirgi Wushishi yayi matukar Farin ciki da godiya akan Wannan abun Alheri da dan majalisa Yayi.

Mai Unguwa ya kara da cewa da yardan Allah zasu ci gaba da ba Hon Abdullahi Idris Garba goyon baya 100% a koda yaushe, Sannan Mai unguwa yayi ma Hon Mai solar Addu’a da Fatan Alheri.

Bayan Bayanin mai Unguwa, Coordinator na mai solar a Wushishi Shehu Ciroma yayi godiya ga mutanen Tashar jirgi akan goyon bayan da suka ba Hon Abdullahi Idris Garba Mai Solar a koda yaushe. Kuma yana mai kara tabbatar masu da Hon. AIG yana shirye ne tsaf don inganta rayuwan Al’ummansa.

Bayan Haka chief imam na Tashar jirgi yayi Addu’a ma kasa da Hon Abdullahi Idris Garba akan Allah yaci gaba da taimakon shi ya kuma bashi ikon ci gaba da adalci akan mutanen yankin da yake wakilta. #AMEEN

Mai Solar ya gode.

Sign:
Bashar Atake

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *