Gidauniyyar Biyafarms Initiative for the Less-privileged Za Ta Tallafawa Almajirai 19,000

Wata gidauniyya mai zaman kanta wacce ake kira da Biyafarms Innitiative for the Less-privileged ta ce a shirye take tsab wajen tallafawa almajirai 19,000 a duk jihohin Arewacin Najeriya 19 ta hanyar horas da su sana’o’i daban daban domin dogaro da kai.

Wanda ya kafa ita wannan gidauniyyar, Alhaji Almustapha Bilyamin, ya bayyana hakan a ranar Talata a yayin ya tattauna da manema na kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a karamar hukumar Karu dake jahar Nasarawa.

Bilyamin ya ce horaswa zai taimaka masu wajen tafiyar da harkokin rayuwar almajirai wanda hakan zai sa su su zanto masu aikin yi har ya kai ga su dauka marasa aiki su ma su basu aiki ta hanyar yin hakan zai kawo ci gaba a kasar.

Ya bayyana irin sana’o’in da gidauniyyar za ta horas da almajiran da su wadanda suka hada da sana’ar kafinta, da kani-kanci, da walda, da tela, da fulamba, da gyaran takalmi da makamancinsu.

“Gurinmu shine mu yiwa almajirai 19,000 rajista domin horas da su sana’o’i daban daban a duk fadin jihohin dake Arewacin Najeriya don inganta rayuwar almajirai

“Shirin na kunshe da kudirin koyawa almajirai sana’o’in hannu daban daban domin su ma su samu damar damawa a harkokin kasuwancin kasar nan

“Hakan zai sa su su tsaya da kansu ba tare da sai sun fita roko ba ko sun dogara ga wani ba wannan zai kara masu mutunci a fuskar al’umma.

“Kudurin ita wannan shirin namu za’a dade ana cin moriyarta wacce za ta horas da almajirai ilimin sana’ar hannu, ta ciyar dasu abinci mai kyau (abinci mai gina jiki) sannan kuma a samar masu da ingantaccen maganin zamani domin inganta rayukansu.

“Shirin kuma ta kudirin dauke almajirai daga titunan Arewacin Najeriya inda mafi yawancin nan ne almajirai suka fi gawa kafin suka shiga Kudancin Najeriya ta hanyar Shigar da su cibiyiyin horas da sana’o’in hannu,” ya ce.

A cewarsa, ya ce a yayin da ake horas da almajiran sana’o’i daban daban gidauniyyar za ta dauki nauyin ciyar dasu abinci ta hanyar hada kai da masu abinci inda kawai za su je ne kawai su karbi abinci,” ya ce.

Bilyamin ya ce gidauniyyar a halin yanzu ta horas da almajirai 120 sana’o’i daban daban a garin Jos, jahar Filato domin dogaro da kai.

“Za mu ci gaba da taimaka almajirai wajen tabbatar da cewa suna cikin tsabta sannan kuma sun samu isashen kula ta bangaren kiwon lafiya,” ya kara da cewa.

Bilyamin ya jaddada cewa gidauniyyar tana nan a kan bakanta wajen ganin cewa ta samarwa almajirai, da marayu da marasa gataingattaccen rayuwa a ko ina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *