Gidauniyyar Biyafarms Initiative for the Less-privilege Ta Raba Buhunan Abinci Ga Marasa Galiho

Wata gidauniyyat wacce ake kira Biya Farms Initiative for the Less-privilege ta raba buhunan shinkafa 300 ga marasa galiho a birnin Jos dake jahar Filato.

Gidauniyyar wacce ta ce ta lashe takobin rage radadin ta hanyar taimakawa al’umma marasa galiho inda ta kewaya a fadin birnin Jos ta tsinto al’umma wadanda ke cikin tsanancin hali ta tallafa masu.

A wani labarin kuma Gidauniyyar ta rabawa mutane 100 kayan abincin dabbobi ga manoma.

Ita wannan gidauniyyar wacce ake kira da suna Biya Farms Initiative for the Less-privilege ba a nan kawai ta tsaya ba tana da wata shiri na musamman da ta shirya don Tallafawa almajirai ta hanyar horas da su sana’o’i daban daban don dogaro da kai ba tare da sai sun fita bara ko sun jira wani taimaka su ba.

Hakazalika gidauniyyar ta ce za dauki nauyin ciyar da wadannan almajirai tare da kula lafiyarsu ta hanyar tabbatar da cewa sun samu ingattacen kula ta kiwon lafiyar zamani. A yanzu haka gidauniyyar na shirin tallafawa almajirai 19,000 wadanda ke fadin jihohin Arewacin Najeriya 19.

Domin Samun Karin Haske Game Da Ita Wannan Gidauniyyar Tare Da Taimaka Ma Ta Wajen Cimma Gurinta Za A Iya Tuntubarsu A Wannan Shafin Na Su: www.biflp.org

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *