Zamfara: Alkalan Da ‘Yan Bindiga Suka Sace Sun Shaki Iskar Yanci

Masu garkuwa da mutane da sukayi garkuwa da wasu alkalai ‘yan jihar zamfara, wadanda suka kwashe kusan wata biyu, sun sami ‘yancin Kansu ta hanyar sakinsu da akayi ayau.

Alkalan biyu,masu suna Salihu Abdullahi da Shafi,u Jangebe, idan ba’a manceba an sace su ne a kan hanyarsu ta komawa jihar Zamfara daga Maradi ta Jamhuriyar Nijar.

Wanda bayan sacesu aka bukaci sai an bada zunurutun kudi har har Naira miliyan Goma ( N10m )kowannensu, sai dai daga bisani wadannan kudaden ba su samu ba.

Sai dai hakan ya sanya ‘yan fashin sun fahimci cewa ba zasu sami wadannan kuden ba duk da barazanar da sukayi da kuma ganin tsawon lokacin da aka dauka a hannunsu sai daga karshe suka kira dangin su tare da neman su kawo duk abinda ya samu a hannunsu domin su sakesu.

Da yake magana da wakilinmu, daya daga cikin ‘yan uwan alkalan da aka saki, mai suna Malam Hassan ya ce “lokacin da‘ yan fashin suka fahimci cewa ba za mu iya biyan miliyan 20 ba, a karshe suka kira mu suka ce mu kawo duk abin da muke da shi a hannun” inji shi.

Hassan ya kara da cewa, “Mun biya miliyan biyu ga alkalan dukkansu su biyu kuma sun sakesu ,a cewarsa, kuma wasu mutane bakwai da ke hannunsu tare da alkalan biyu suma sun biya kudade daban-daban kuma an sake su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *