Masarautar Zazzau: Kotu Za Ta Raba Gardama Yau

A yau Juma’a ne Shida ga watan Nuwamba, 2020, babbar Kotun jihar Kaduna za ta saurari shari’ar nadin sarkin Zazzau, da kuma yanke hukunci akan makomar rawanin sabon Sarki Ahmad Bamalli.

Wannan kotu da ke zama a Zaria, jihar Kaduna, zata saurari ƙarar da daya daga cikin ‘ya’yan Sarakunan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu da ya shigar a gaban ta.

A ranar Laraba, kotu ta saurari Lauyoyi masu shigar da kara da kuma masu kare wanda ake zargi.

Kotu ta sa ranar sanar da makomar sabon sarkin Zazzau Bayan an yi zama a ranar 4 ga watan Nuwamba, Alkali mai shari’a Kabir Dabo ya dage karar zuwa yau, ya ce a ranar Jum’a kotu za ta yanke hukunci.

Iyan Zazzau, Aminu ya roki Alkali ya bayyana shi a matsayin sabon Sarkin Zazzau, sannan ya yi fatali da nadin da gwamnati ta yi wa Ahmad Bamalli.

Lauyoyin Bashir Aminu sun kuma nemi alfarmar kotu a dakatar da bikin nadin sabon Sarkin Zazzau, sannan a hana mika wa Sarkin sandar girma.

Iya ya shigar da kara ne ta hannun Babban Lauya Ustaz Yunus SAN a kotun da ke Dogarawa, Sabon Gari, Kaduna.

Idris Aliyu shi ne Lauyan da ya tsayawa gwamna da sakataren gwamnati da kwamishinan shari’ar Kaduna, ya kuma kare gwamnati a zaman da aka yi.

An ruwaito Lauyan da ya tsaya wa Kwamishinan harkar masarautu shi ne Kenechukwu Azioyo. Lauyoyin sun roki ayi fatali da karar babban basaraken.

Idan baku mance ba Iyan Zazzau ya na ikirarin masu nadin sarki sun mika wa gwamna Nasir El-Rufai sunansa a matsayin magajin Shehu Idris.

Mutane 10 ake kara a wannan shari’a, daga ciki har da shi El-Rufai, babban Lauyan jihar Kaduna; Majalisar Sarakunan Kaduna; Majalisar Masarauta. Sauran su ne: Wazirin Zazzau, Fagacin Zazzau, Makama Karamin Zazzau, Limamin Juma’an Zazzau, da Mai martaba Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *