Ku Dakatar da Buhari Daga zuwa Yawon ganin Likita – Kwamitin Majalisar Dattawa Ya Bayyanawa Jami’an Gidan Gwamnati

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Majalisar Dattawa ta fada wa jami’an gidan Gwamnatin Tarayya da su hana Shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa kasashen waje domin neman lafiya don tabbatar da cewa asibitin fadar Shugaban Kasa ya fara aiki a bana.

Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tarayya da Harkokin Gwamnati ya ba da wannan gargadin Ne lokacin da Babban Sakatare Tijani Umar, ya bayyana a gaban kwamitin don kare kiyasin kasafin kudin 2021.

Jami’in na Fadar Gwamnati ya gabatar da kasafin kudi na N19.7bn, daga ciki an bayar da N1.3bn don asibitin gidan gwamnati.

Da yake tsokaci game da shawarar Shugaban kwamitin majalisar dattijai, Sanata Danjuma La’ah, ya ce kwamitin zai amince da kasafin kudin asibitin fadar gwamnati amma ya dage cewa shugaban kasar da sauran manyan mukarraban gwamnatinsa ba za su sake tafiya kasashen waje don duba lafiyarsu ba.

Ya kuke gani?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *