Gwamnatin Katsina Za Ta Dau Nauyin Duk Yaran Da ‘Yan Ta’adda Suka Halaka A Fadin Jahar

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari yasha alwashin cewa Gwamnati zata dauki nauyin dukkanin yaran da barayin daji suka kashe wa iyaye a rikice-rikicen da jahar ta fuskanta.

Gwamnan ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Yan banga na Kasa Dr.Muhammad Usman fadar gidan gwamnatin jihar Katsina.

Masari ya kara dacewa gwamnati zata kafa kwamiti da zai zagaya a garuruwan da abin ya shafa domin zakulo yaran tare da basu kulawa ta musamman.

A cewar sa yin hakan ya zama wajibi a taimaki rayuwar yaran a fadin jahar, inda yace idan Gwamnati ba ta dauki wani mataki ba to nan gaba da yaran za’a yi yakin.

Gwamnan ya kuma yaba akan yadda yan bangar suke bada gagarumar gudunmuwa wajen samar da tsaro a jihar Katsina dama kasa baki daya, tare da yin kira a garesu dasu rika hannanta duk wanda suka kama ga Yan Sanda domin bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *