Gwamnonin Arewa Sun Bar Jaki Sun Koma Dukan Taiki – Matasan Arewa

Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa 19, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Nastura Ashir Shereef, sun bayyana taron da kungiyar gwamnonin Arewa suka gudanar tare da Sarakunan Arewa kwanan nan a Kaduna, a matsayin wani zama da ya yi hannun riga da muradun jama’ar Arewa.

AdvertisementScroll to Continue
Matasan sun bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da suka kira wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake garin Kaduna.

Matasan sun bayyana cewar babban abin mamaki ne da takaici a taron gwamnonin Arewa, inda gaba ɗaya basu yi magana akan matsalar da ke addabar yankin ba na taɓarɓarewar tsaro da garkuwa da mutane, sai kawai suka ɓige da surutu akan maganar Zanga-Zangar Endsars da batun Soshiyal Midiya.

“Irin waɗannan halaye da gwamnonin Arewa suke nunawa shine ya ke sanyawa ake wulakanta ‘yan Arewa musanman a kudancin ƙasar, ake ɗaukar ‘yan arewa a matsayin wawaye marasa alkibla”.

Matasan na Arewa sun ƙalubalanci gwamnonin na Arewa da yin koyi da gwamnan jihar Ribas Wike wanda ya fito fili ya la’anci Ƙungiyar Tsagerun Inyamurai IP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *