EndSARS: Shugaban ‘Yan Sanda Ya Umarci ‘Yan Sanda Da Komawa Aiki

Shugaban rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Muhammad Adamu, ya umarci ‘Yan sanda da su koma bakin aikinsu cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban Yan Sandan ya ƙara da cewar, kada su kuskura su bar bata-gari da ‘yan ta’adda su cigaba da yin yadda suka ga dama, su yi damara na maganin duk wani tsagera da ɗan ta’adda a faɗin ƙasar.

Muhammad Adamu ya musanta labarin masu zanga-zangar EndSARS da aka ce ‘yan sanda sun kai musu farmaki, har wasu sun ji rauni ko rasa rai.

Shugaban ya yi wa ‘yan sanda jawabi a hedkwatar Edo da ke GRA Benin, lokacin da yake ba ‘yan sanda kwarin guiwa a kan konannun ofisoshin su da aka kona a jihar Edo.

Sifetan ‘Yan Sandan wanda ya samu rakiyar mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, mataimakin sifeta janar na ‘yan sanda, Shola David da kwamishinan ‘yan sanda, Babatundu Kokumo, ya bayyana cewar:

“Farmakin da aka kai wa ‘yan sanda da ofisoshinsu an yi ne don a wulakantasu, kuma a nuna musu cewa mutane ba sa mara musu baya.

“‘Yan sanda jami’ai ne na musamman saboda an horar da su musamman don taimakon al’umma.

“Shiyasa duk da harin da aka kai mu ku, kuka share su, kuma ku ka tsaya kai-da-fata wurin taimakonsu. “Ina kara ba ku kwarin guiwa, kada ku sare, ku tabbatar kun cigaba da tabbatar da tsaro a wurare daban-daban.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *