‘Yan Sanda Sun Kashe Wani Dan Fashi Da Makami A Katsina

Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta ce ta yi nasarar harbe wani dan fashi da makami a kan hanyar Bakori zuwa Kabomo, a Karamar hukumar Bakorin jahar.

A cikin wata takarda daga mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Gambo Isah, ta ce ‘yansandan sun samu rahoton ‘yan fashi sun tare hanyar da misalin karfe 8:30 na daren Talatar nan data gabata.

Takardar kara dacewa Shugaban ‘yansanda na karamar hukumar Bakori shine ya jagoranci tawagar ‘yansanda suka isa wurin, inda aka fara musayar wuta, wanda a dalilin haka, suka samu nasarar bindige daya daga cikin ‘yan fashin.

Gambo Isah wanda yace ‘yansanda sun kuma yi nasarar kwace bindiga kirar ta gida, ya ce ana cigaba da gudanar da bincike akan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *