Buhari Ya Kewaye Kansa Da Mugayen Mutane, Suna Ta Gaya Masa Karairayi

Shugaban cocin Adoration Ministry dake a Jahar Enugu Ejike Mbaka yace Ana gayawa Shugaba Muhammadu Buhari karairayi, daga Mutanen da ke kewaye da kansa.

Mbaka ya kuma zargi Jami’an tsaro da kashewa, tare da jibge gawarwakin Wasu masu Zanga-zangar EndSARS a tabkin Onyeama dake jahar.

Ya bayyana haka a ranar Lahadi, inda ya bukaci Buhari daya nemi yafiyar Kasar nan, a madadin sa da wadanda ya gada, wanda suka kawo ma Najeriya wahalhalun da take ciki.

Ya kuma yi zargin cewa, Matasa da dama an kama su, an kuma tsare su a gidajen Gyaran Dabi’a na Jahar dama na sauran kasa, inda ya bayyana cewa Shuwagabannin Najeriya ya kamata ace suna cikin wadannan wurare ba matasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *