Bidiyon Rahama Sadau yayin da ta nemi afuwa cikin kuka kan ɓatancin da aka yi wa Musulunci kan hotunanta

Tauraruwar fina-finan Hausa Rahama Sadau ta nemi gafarar masoya, da ‘yan uwa da abokan arzikinta, dangane da martanin da wani mai bibiyarta ya yi a kan wasu hotuna da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta.

Jarumar ta bayyana cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram sanye da hijabi, cikin kuka da murya mai rawa, tana neman a yafe mata.

”Duk wanda ya sanni, kuma yake bi na, ya san cewa ba zan taɓa yin wannan abu har cikin zuciyata ba, hasali ma ban san abun da ya faru ba sai da aka kira ni” a cewarta.

A ranar Litinin ne sunan Rahama Sadau ya fara waɗari a Twitter, inda aka ambace shi sau fiye da 10,000, bayan hotunan da ta tauraruwar ta saka suka ja hankalin masu bibiyarta da kuma masu amfani da Twitter musamman daga arewacin Najeriya.

Daga baya tauraruwar ta ce sam “ba da yawunta ba” aka dinga kalaman ɓatancin da wasu suka riƙa yi biyo bayan wallafa wasu hotuna da ta yi a shafukan sada zumunta.

Kalaman na tauraruwar fina-finan Kannywood da Nollywood na zuwa bayan wasu sun yi ta amfani da maud’in #AssistantAllah a Twitter da zummar kare ta daga sukar da wasu ke yi mata kan bayyana jikinta a sabbin hotunan da ta saka.

Jarumar ta ce a matsayinta na Musulma, ba za ta taɓa yin wani abu da ta san zai janyo batanci da Anabi Muhammad ba, da alama tana magana ne kan wani da ba musulmi ba da ya alakanta shigar da ta yi a hotunan da addinin musulunci, abin da yasa masu bibiyarta ke zargin ita ce ta janyo faruwar hakan.

A cikin sabon bidiyon neman afuwar da ta nema a ranar Talata, Rahama ta ce ”Ko ma mene ne dai ƙaddara ta riga fata” in ji Sadau, ”amma dai ina mai bai wa ɗaukacin al’umma hakuri, don Allah a yi hakuri” ta ci gaba da kuka.

Taurari a ciki da masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood da dama sun fito sun yi Allah-wadai da abin da ya faru.

Ko da a shekarar 2016 ma wani bidiyo da ta taka rawa a cikinsa tare da mawakin gambarar nan Classic ya janyo ce-ce-kuce a shafukan sada zumunta, inda wasu ke cewa abin da ta yi a bidiyon ya saɓa da tarbiyyar a’ummar Arewacin Najeriya.

Madogara: BBC HAUSA

kalli Bidiyon a kasa;

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *