Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Ya Kai Ziyara Wajen Da Ake Baiwa Jami’an SWAT Horo.

Sabuwar rundunar ‘yan sanda da ake kira (SWAT) a ranar Litinin ta fara horar da ma’aikata sama da 400 a Kwalejin ‘Yan sanda da ke Eggon a Jihar Nasarawa.

Ministan Harkokin ‘yan Sanda na ƙasa Muhammad Dingyaɗi ne ya halarci wurin Horon Domin Duba yadda Horon ke Tafiya Cikin Nasara, inji shi.

A jawabinsa na bude taron, Ministan ya ce ya yi farin ciki da ci gaban da ma’aikatan ke samu tare da umartar su da su zama masu koyi da al’umma.

Ya kara da cewa “Na yi imani a karshen wannan atisayen za ku fito ne a matsayin jami’an ‘yan sanda masu kwazo da himma wadanda za su yi daidai da aikin da muka sanya ku”

”Sabon aikin ku a matsayin maye gurbin SARS shi ne fuskantar kalubalen fashi da makami da sauran laifuka a fadin kasarnan.”

Ya kuma ce zamu kawo sauye-sauyen zamani sannan ya shawarci ma’aikata da su kiyaye ka’idojin dimokuradiyya da ‘yancin dan adam yayin da suke kan gabatar Da aikinsu.

Ministan ya kara tabbatar wa ma’aikatan shirye-shiryen Shugaba Muhammadu Buhari don inganta walwalarsu da sauran ƙunshin da aka yi musu alkawari.

Ma’aikatan da suka haura 400 sun kwashe makonni suna samun horo a kwalejin, wanda shine wuri na biyu da ake horar da ma’aikatan SWAT a kasarnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *