Maganin Nankarwa (Stretch-Marks)

Nankarwa shine irin wannan zanen da yake fitowa a cikin mace da zaran ta fara haihuwa ko kuma in tayi kiba
A ciki mace ya kan fitowa ya sanya fatar cikin duk ta yamuste
ana amfani da man dodon kodi a shafa a ciki,yana gyara fatar ciki ta koma kamar ba ta haihu ba;
● man kadanya
● man zaitun
● Lemun tsami
Yadda Ake Hadawa:
Ki hada man kadanya da man zaitun guri daya, ki matsa lemun tsami a kai, amma ba da yawa ba,ki matsa sosai sannan sai ki dinga sharewa ki yawaita yi
Yadda Ake Amfani Da Shi:
Ana shafa zuma farar saka da daddare, idan zaki kwanta barci da safe sai ki samu ruwan dimi ki wanke.