Hotunan Nuna Tsiraici: Hukumar Ladabtarwa Ta Kannywood Za Ta Hukunta Jaruma Rahma Sadau


Hukumar Ladabtarwa ta masanaantar shirya fina-finan Hausa na Kannywood sun shelanta cewar zasu dauki Mataki a kan Jaruma Rahma Sadau.

Ya Litinin da misalin karfe 4:25, shafin KANNYWOOD ya wallafa sakon a shafin sa kamar haka “Zamu Iya kokarin mu domin daukan mataki akanta kuma muna kira ga masoya #kannywood dasu daina yi mata comments ko like idan ta saki irin wannan Kuma da kanku masu kallo zaku iya bamu gudunmawa wajen ladabtar da ita idan zakuyi unfollowing dinta a Instagram/Facebook da shafin Youtube”

A daren Jiya Lahadi ne Jaruma Rahma Sadau ta wallafa wadan su zafafan Hotuna a shafinta na Instagram wanda suka jawo cece-kuce tun daga daren Jiya zuwa yau Litinin.

Jaridar Dimokuradiyya, ta ruwaito cewar masanaantar ta Kannywood tayi Amai ta lashe ne don su ma sun wallafa hotunan a shafin su, yanzu kuma sun zo suna Allah wadai.

Wannan bashi bane karo na farko da Jaruma Rahma Sadau take jawowa kanta maganganu marasa dadi, don har yanzu baa dauki dogon lokaci ba da Masaantar ta Kannywood ta yafe mata laifukan ta.

.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *