‘Yan Najeriya Sun Wadatu Da Lantarki – Ministan Lantarki

“Babu wani Gari ko wata Unguwar a faɗin Najeriya da ba sa samun hasken wutar Lantarki a kullum, saidai idan suna da matsalar Taransifoma ko kuma turakun wuta basu kai inda suke ba”.

Ministan wutar lantarki, Injiniya Saleh Mamman ya ƙara da cewa babu wani ɗan Nijeriyan da zai ce ba a samu canji a bangaren wuta ba karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

A hirar da yayi da BBC Hausa, Saleh Mamman ya ce kashi 80 zuwa 90 na masu samun wutan lantarki zasu tabbatar an samu canji na wutan lantarki.

Ya ce gaba daya Najeriya an samu karin wutan lantarki karkashin gwamnatin Buhari.

Ya kara da cewa babu gari ko anguwar da zata ce ta kwana daya ba’a kawo wuta ba sai da idan wani abu ya lalace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *