Wata Tankar Man Fetur ta kama da wuta kusa da ofishin Gwamnan Ogun

Wata Babbar Mota mai dauke da Kimanin Litar Man Fetur Dubu 50,000 ta kama da wuta a gaban ofishin Gwamnan Jahar Ogun Oke Mosan dake Abeokuta.

Lamarin dai ya farune a yau din nan Asabar, inda tankar ke tahowa daga Ijora ta Jahar Lagos kan hanyar Adatan a cikin garin Abeokuta.

Direban Tankar wanda ake kira da Nurudeen Yusuf ya gayawa Manema Labaru cewa, shi da yaran motar nasa sunji fashewar wani abu a cikin injin Motar, wanda hakan ya haddasa tashin wutar.

Shugaban tawagar Hukumar kiyaye Gobara a lamarin Sodiq Atanda yace an dauki tsawon lokaci ana kawo dauki kafin a kashe wutar.

Atanda yace “ba dan inda lamarin ya faru yana kusa da Ofishin su” da kuma daukin gaggawa da Jami’an mu suka kawo, da Lamarin ya yi muni sosai”

Ya kuma koka akan yadda Duk Girman Motar amma bata dauke da Abin Kashe Gobara wato-Fire Extinguisher

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *