Gwamnan Legas Ya umarci Dukkanin Ma’aikata Dasu Dawo Bakin Aiki

Gwamnan Jahar Legas Babajide Sanwa-Olu ya umarci dukkanin Ma’aikata tun daga Mataki na 1 ya zuwa 12 dasu dawo bakin aikinsu daga ranar Litinin 2 ga watan Nuwanbar 2020

Wannan na kunshene a cikin wata Sanarwa da Shugaban Ma’aikatan Jahar Hakeem Muri-Okunola ya fitar a yau.

Idan dai ba’a manta ba, an umarci dukkanin Ma’aikatan tun daga watan Mayu, dasuyi aiki a gida a matsayin wani mataki na magance yaduwar Annobar COVID-19 a jahar.

Domin tabbatar da bayar da tazara a Ma’aikatu da Sassan Gwamnati, aka umarci Akantoci na wuraren dasu dauki sunaye tare da tabbatar dacewa an bi dukkanin Dokokin Kariya akan cutar Corona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *