Sokoto: Wamakko Ya Shirya Addu’ar Samun Tsaro A Najeriya

Tsohon gwamnan jahar Sokoto Dr Aliyu Magatakarda Wamakko ya shirya addu’a ta musamman a yau Juma’a a gidan sa dake Gawon-Nama jim kadan bayan dawowarsa daga birnin tarayya Abuja.

Sanata Wamakko ya shirya addu’ar ne domin neman dauki daga wajen Allah madaukakin sarki na matsalolin da ke addabar kasar mu Najeriya wadanda suka hada da matsalar tsaro, zanga-zangar EndSars, garkuwa da mutane, kashe-kase da sauran abubuwa.

Hakama Sanata Wamakko yayi kira ga matasan Najeriya da su guji shiga duk wata zanga-zangar wadda zata haifar da tashin hankali ko asarar dukiya.

Daga karshe Sanata Wamakko ya roki Allah madaukakin sarki ya kawo mana karshen dukkanin musifun da ke addabar kasar mu Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *