Shinkafar Da Aka Sace Bada Ofishina Suke Ba – Inji Ministar Jin Kai

Hukumomin Ma’aikatar Jin Kai ta Tarayya, da Kauda Bala’i da Ci Gaban Jama’a a ranar Juma’a sun tabbatar da cewa jigilar shinkafar da aka sata daga wani sito da ke Legas ba na Ma’aikatar ba ce.

Mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga Ministan Harkokin Jin Kai, Nneka Ikem Anibeze ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar a Abuja.

Anibeze ta bayyana hakan ne yayin da take maida martani game da rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ta yi zargin cewa kudaden da aka samu na COVID-19 ba a ajiye wani kaya da su ba balle ma har a sace su.

An sanar da Ma’aikatar Kula da Bala’in da ke Kula da Harkokin Jin Kai da Ci Gaban Jama’a game da sakonnin da ke tafe a kafafen sada zumunta da ke nuni da cewa kayan da aka samu na COVID-19 da aka samu a wani dakin ajiyar na Legas daga ma’aikatar suke.

Wannan ba komai bane face tarin karya, Inji ta.

Hotuna da bidiyon da aka dauka a dakin ajiyar kayayyakin sun nuna cewa buhunan shinkafar da wasu abubuwa a bayyane suke ba na Ma’aikatar ba ne.

“CA-COVID shine gajeren tsari na Coalition Against COVID-19, wani kwamiti mai zaman kansa wanda zai jagoranci hadin gwiwa tare da Gwamnatin Tarayya, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya NCDC da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tare da nufin yaki da Covid-19 a Najeriya.

“Ma’aikatar Tarayya ta Harkokin Jin Kai da Kula da Bala’i da Ci Gaban Jama’a ba su sayi, ko saukaka rarraba kayan agaji a karkashin shirin Ca-Covid ba.

Ta ce, “Saboda haka, ma’aikatar na son sanar da jama’a cewa ba ruwanta da kayayyakin da aka gano a cikin wannan rumbun na Legas,”

To na waye kenan?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *