Bauchi: Uwargidan Gwamna Ta Raba Tallafin Kayan Abinci

Uwar gidan gwamnan jihar Bauchi Aisha Bala Abdulkadir Mohammed taja hankalin iyaye da suci gaba da tarbiyan yayansu domin samun ci gaba tare da zaman lafiya mai dorewa

Tayi wan nan kiran ne a lokacin taron da ta shirya na addu’oin zaman lafiya ma kasa, da kuma raba kayan abinchi ga makarantun Islamiyya a jihar Bauchi.

Aisha Bala tace babu al’ummar da zata ci gaba cikin rudani da tashin hankali, saboda haka iyaye suna da jan aiki ta wajen kulawa da yayansu,

“Irin wan nan tashin hankali a sanadin zanga- zanga, dole ne matasa su nemi hanyan zama lafiya, saboda haka kullun muke amfani da masu ilimi su bamu sha’warwari tare da nasiha ma al’ummar baki daya, lokaci yana tafiya kuwa ya kuma ga Allah”

Kana ta roki malamai, sarakuna, shuwagabbani a mataikai dabam-dabam da arika ma mutane nasiha da kuma jin tsoron Allah domin samu daidaito tsakani bangarori biyu ko da gwamnati ne, tace dole sai anyi hakuri da juna.

Shugaban ma’aikatan na gidan gwamnati Dakta Ladan Salihu wanda ya wakilci gwamnan jihar a wajen addu’ar, yace Gwamnan ya nuna alhinin sa gami da abin da ke faruwa a wasu sassan Najeriya, “duk lokacin da aka samu son zuciya to dole a samu akasin zaman lafiya”

Ya kara da nusar da mutane da aci gaba da hakuri sabo da tashin hankali baya kawu chi gaban kasa, sai dai koma baya, yace muna bukatar yanayi na addu’a, ga Allah, sa annan ya yabawa uwargidan gwamnan jihar kan ayyukan ta na alheri, da kuma addu’ar ci gaba da tallafa ma marasa galihu da takeyi.

Ladan Salihu ya kara da cewa “ita addu’a kariya ce kuma takubi ce ga dukkanin mumini, yace duk halin da mutum ya sami kansa to ya godewa Allah, daboda shi yake da iko akan dukkan komai”

Malamai ne da dama suka halarci taron addu’ar, kuma sun yaba da kokarin uwar gidan gwamnan don shirya wan anan taron yin addu’oi saboda halin da kasa take ciki.

Bugu da kari Aisha Bala wadda ita ce Sarauniyar Bauchi ta raba ma yan makaratun Islamiyya kayan abinci domin rage radadin tattalin arziki.

Malam Yahuza Bauchi ya gudanar da karatun Alqur’ ani mai girma, tare da gudanar da addu’oi na musamman domin samun zaman lafiya a jihar Bauchi, da ma kasa baki daya daga bakin maluman da suka halarci taron

Daga Adamu Shehu Bauchi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *