An Gurfanar Da ‘Yan Sanda 31 A Gaban Kotu Kan Take Hakkin Mutane

Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Legas ta fitar da sunayen ‘yan sanda 31 da a yanzu haka ake musu shari’a kan take hakkokin bil’adama, wadanda suka hada da kisan kai, yunkurin kisan kai, kisan kai da gangan, jiwa mutane Munanan Raunuka.

An gurfanar da ‘yan sandan da aka zayyana Daban ko kuma a kungiyance a gaban Babbar Kotun Jihar Legas tsakanin 2012 zuwa 2020. Wasu an gurfanar da su, yayin da wasu ke jiran gurfanar wa.

A jerin sunayen akwai Sufeto Surulere Irede, Sgt. Sunday Ogunyemi da Kofur Hezekiya Babatunde, wadanda ke zaman kotun tare bisa zarginsu da kisan kai a gaban Mai Shari’a Ogunsanya; kazalika da Sgt. Segun Okun da Kyaftin Adekunle Oluwarotimi, wadanda ake tuhumar su tare da kisan kai da kuma yunkurin kisan kai a gaban mai shari’a Nicole Clay.

Sauran wadanda ake tuhuma daban-daban sune Ogunyemi Olalekan (kisan kai), Sgt. Gbawuan Isaac (mummunan rauni a jiki), Aminu Joseph (kisan kai), Sgt. Alechenu Benedict (fashi da makami), Sgt Adebayo Abdullahi (kisan gilla ba da niyya ba), Sufeto Mohammed da wasu mutum biyu (fashi da makami), Matthew Chansi (kisan kai), Adamu Dare (kisan kai), Sgt. Mark Argo da wasu biyar (makirci da fashi da makami), da Kofur Pepple Boma (kisan kai).

Hakanan a cikin jerin akwai Insp. Emmanuel Akpodana (yunkurin kisan kai), Emmanuel Uyankweke (kisan gilla ba da gangan ba), Akanbi Lukmon (kisan gilla ba da niyya ba), Edokhe Omokhije (kisan kai), Afolabi Saka (kisan kai), Monday Gabriel (kisan kai), Yahya Adesina (kisan kai ba da niyya ba) da kuma Aremu Musiliu (kisan kai) ).

Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Legas, Mista Moyosore Onigbanjo (SAN), wanda ya fitar da jerin sunayen, ya ce, “Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Legas ta himmatu kan lokaci zuwa gurfanar da wadanda aka lissafa da kuma masu alaka da cin zarafin’ yan sanda.

Kuma Ina kira ga jama’a da su ci gaba da bin kadin wadannan hukunce-hukuncen don tabbatar da amfanin jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *